in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaman addini a jihar Kano sun himmatu wajen sanar da jama`a mahimmancin layya a tsarin addinin musulunci
2013-10-15 16:25:46 cri
Yau Talata 15 ga watan Oktoba ne al`ummar musulmin duniya suna gudanar da bikin babbar sallah.

Wakilinmu dake Kano Garba Abdullahi Bagwai ya shirya mana rahoto na musamman game da mahimmancin layya ga al`ummar musulmi a lokacin babbar sallah.

Malam Adam Umar shi ne shugaban kungiyar dalibai musulmi ta tarayyar Najeriya reshen jihar Kano ya yi karin haske game da layya, inda ya ce ana yin layya ne kwana guda bayan tsaiwar arfa a daidai 10 ga watan zulhijja watan karshe na kalandar musulunci.

Shi kuma Sheik Aliyu Yunus babban limamin masallacin Usman bin Affan dake unguwar Gadon ya ce kowane musulmi da yake da halin yin layya zai yanka dabbarsa ne bayan liman ya yanka nasa wato jim kadan da kammala sallar idi.

Ya kuma lasafto nau`in dabbobi uku da Allah ya yi umarni a yanka a lokacin babbar sallah, wadanda suka hada da Rakuma, Shanu, Rago, Tunkiya ko Akuya.

A lokacin da nake jin ta bakinsa game da irin alfanun dake tattare da yin layya Sheik Bashir Abdulsalam babban limamin masallacin jumma`a na uhud dake birnin Kano, ya ce babu shakka akwai alkairai da dama ga wadanda suka samu damar yin layya .

Ya ce layya za ta kara kusantar da musulmi ga ubangiji, kuma layya na baiwa jama'a damar yin zumunci ta hanyar yin sadakar nama ga wadanda ba su samu damar yin layyar ba.

To kasancewar dabbobi a bana suna tsada sosai a jihar Kano, na ji ta bakin masu sana`ar sayar da dabbobi yadda cinikin dabbobi yake a bana. Da yawa daga cikin masu wannan sana`a sun ce matsalar karancin kudi a hannun jama`a shi ne ya sanya kasuwar bana ba ta da kyau.

Su kuma masu saya fa me za su ce game da yadda farashin dabbobin ya yi tashi gauron zabi? Inda suka yi kira ga masu sayar da dabbobi da su yi la`akari da halin da ake ciki na rashin kudi wajen rage farashin dabbobin nasu.

A halin yanzu dai jami`an tsaro a jihar Kano sun dauki tsauraran matakan tsaro a sassa daban daban na birnin Kano domin tabbatar da ganin an gudanar da shagulgulan sallah lafiya. (Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China