Shugaban Sin ya nuna juyayinsa ga wadanda suka rasu sakamakon tarwatsewar jirgin saman fasinjan Malyasia a kasar Ukraine
Jiya Jumma'a 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari game da faduwar jirgin saman fasinjan na kasar Malyasia a kasar Ukraine, yayin da yake ganawa da manema labarai tare da shugabar kasar Argentina Cristina Fernandez de Kirchner a babban birnin kasar Argentina, Buenos Aires.
Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta nuna bacin ranta kan faduwar wannan jirgin sama a gabashin kasar Ukraine, kuma ya nuna juyayinsa matuka ga wadanda suka rasa rayukansu cikin wannan hadari. Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata a gudanar da bincike yadda ya kamata don gano dalilan afkuwar wannan hadari cikin gaggawa. (Maryam)