Wani jirgin saman fasinja na kamfanin Malaysia Airlines dake dauke da fasinjoji 280 da kuma ma'aikatan jirgin 15 ya tarwatse a Ukraine kusa da iyaka da Rasha, in ji kamfanin dillancin labarai na Interfax.
Wani jirgin sama kirar Boeing 777 na kamfanin Malaysia Airlines, wanda ya taso daga birnin Amsterdam zuwa birnin Kuala Lumpur ya fara saukowa kasa kasa zuwa kilomita 50 daga sararin samaniyar kasar Rasha, kuma ya kama da wuta a kasa a Ukraine, in ji wata mijiyar jiragen sama da Interfax ya rawaito.
Jirgin ya bace daga na'urar rada a nisan mita 10000 a sararin samaniya, sannan ya fado kusa da birnin Chakhtarsk dake yankin Donetsk na kasar Ukraine, in ji Interfax tare da ambato kalaman hukumomin Ukraine cewa, za su aiki da doka kan wannan lamarin. (Maman Ada)