Gwamnatin kasar Sin ta bayyana bacin ranta game da tarwatsewar wani jirgin saman kamfanin Malaysia Airlines a kasar Ukraine, kuma ta fara bincike kan sanin ko akwai 'yan kasar Sin a cikin wannan jirgi, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar Alhamis a Brasiliya.
Mun yi matukar kaduwa game da samun labarin cewa, wani jirgin fasinja MH17 na kamfanin Malaysia Airlines ya tarwatse a gabashin Ukraine. Muna isa da ta'aziyarmu da jajantawarmu ga iyalan da wannan hadari ya rutsa da 'yan uwansu. Kuma muna fatan za'a gano dalilan afkuwar wannan hadari cikin gaggawa, in ji mista Qin Gang, dake rakiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping a rangadin da yake a shiyyar kudancin Amurka. (Maman Ada)