in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha na zargin Kiev da harbo jirgin Malaysia
2014-07-18 21:08:50 cri
Ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta bayyana cewa, na'urorinta sun ga makaman kakkabo jirage na kasar Ukraine na shawagi a yankin sararin samaniyan da aka harbo jirgin saman kasar Malaysia samfurin MH 17.

A cikin wata sanarwar da sashin watsa labarai na ma'ikatar tsaron Rasha ya fitar ya bayyana cewa, an girke makamai masu linzami kuma masu cin dogon zango na kasar Ukraine guda biyu samfurin S-200 da kuma makaman kakkabo jiragen sama guda uku na BUK-M1 masu cin matsakaicin zango a yankin da hadarin ya faru.

Masu nazarin harkokin sojan kasar Rasha, sun yi hasashen cewa, kowane daga cikin wadannan makamai guda uku suna iya harba makamai masu linzamin da zai iya kakkabo jirgin.

A halin da ake ciki, hukumar tsaron kasar Ukraine ta karyata hannun dakarun ta cikin wannan lamari, kuma ta ce babu daya daga makamanta masu linzami na kakkabo jiragen sama da suka bata.

Har yanzu dai ba a san musabbabin faduwar jirgin na Malaysia dake dauke da fasinjoji 298 a gabashin Ukranie ba, amma ana zargin Kiev da mayakan da ke gabashin kasar da hannu wajen harbo jirgin na Malaysia. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China