Mista Koffi dake bayani bayan wata ganawa tare da ministocin harkokin waje da na tsaron kasashen biyu domin mai da hankali kan wannan batu ya nuna cewa muhimmin abu shi ne na tabbatar da zumunci da dangantakar makwabtaka tsakanin Guinee da Cote d'Ivoire.
Bangarorin biyu sun zabi hanyar daidaita rikicinsu bisa teburin shawarwari kuma suna mai da hankali sosai, in ji mista Koffi.
A nasa bangare, ministan tsaron kasar Guinee Loceni Fall ya nuna cewa, iyakokin Afrika an yi su ne kara zube. Al'ummomin kan iyakoki sun kasance daya, suna amfani da harshe guda kuma suna da al'adu guda, in ji mista Fall.
Haka kuma ya sanar wata ganawa a nan gaba tsakanin hukumomin kasashen biyu domin kafa wani kwamitin kwararru da za'a dora ma nauyin shata iyaka.
A halin yanzu, hukumomin kasashen biyu na ci gaba da yawaita aika sakonnin kwantar da hankali zuwa al'ummominsu dake kan iyakar. (Maman Ada)