Kwamitin sulhu na MDDr wanda ya gudanar da wani taro kan halin da kasar ta Cote d'Ivoire ke ciki a jiya Laraba, inda ya zartas da wannan kuduri da zai kara wa'adin aikin tawagar zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2015.
Ana dai fatan wannan tawaga za ta bada gudummawa ga mahukuntan kasar Cote d'Ivoiren wajen shirya zaben shugaban kasar da ke tafe cikin shekarar ta 2015. Baya ga taimakawa bangarori daban daban na masu ruwa da tsaki a fagen shafar siyasar kasar wajen gudanar da shawarwari. Koda yake dai batun tabbatar da tsaron rayukan fararen hula shi ne aiki mafi muhimmanci ga tawagar. (Zainab)