Yayin da yake amsa tambayoyin da manema labaran kasar Faransa suka yi masa a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, Mr.Duncan ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da manufofin ba da gatanci da dama ga kasar Cote d'Ivoire kan ayyukan hadin gwiwar tattalin arzikin dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce, gwamnatin kasar Sin da wasu bankunan kasar Sin sun samar da taimakon kudi da manufofin ba da gatancin rancen kudi ga kasar Cote d'Ivoire don samar da kayayyakin more rayuwa ga la'ummar kasar.
Ya kuma kara da cewa, bai kamata kawai kassahen yammacin su zargi masu zuba jari na kasar Sin dangane da samun albarkatun ma'adinai a nahiyar Afirkaba, ya ce, Sinawa sun taimaka mana wajen raya kasarmu. (Maryam)