A ranar 19 ga wata, gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta zartas da wani shirin yaki da hakar ma'adinan zinari ba bisa doka ba a kwanakin baya, inda aka bukaci bincike kan dukkan wuraren da ake hakar zinari a kasar, tare da yin kididdiga kan yawan ma'aikatan masu hakar zinari da kuma kayyade ayyukan da ake gudanar a ma'adinan. An ce, za a rufe dukkan wuraren hakar zinari da ba su da izni, kana za a korar ma'aikatan da ba su yi rajista ba. Game da wuraren hakar ma'adinan da suka samu izni, ya zama wajibi su rika aiki bisa doka, da kuma yin amfani da fasahohin da suka dace da ma'aunin kiyaye muhalli da gamayyar kasa da kasa ta amince da su.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ko da yake kamfanonin hakar ma'adinai na kasa da kasa da dama sun samu iznin hakar zinari a kasar Cote d'Ivoire, amma akwai ma'adinai da dama dake arewaci, tsakiya, yammaci da kuma kudancin kasar dake amfani da fasahohin gargajiya. (Zainab)