Erdogan ya bayyana daukar wannan mataki ne yayin zaman shawarwari da ya yi da shugaban kasar Abdullah Gül a daren ranar Laraba 25 ga watan nan.
Wannan mataki dai ya zo bayan zanga-zangar da masu adawa da gwamnatin kasar suka yi a wannan rana da dare a manyan biranen kasar 10 ciki har da Istanbul, birni mafi girma a kasar, da babban birnin kasar Ankara, da birnin Izmir da ke bakin tekun Aegean, inda masu zanga-zanga suka bukaci a kawo karshen gwamnatin kasar da ke karkashin shugabancin firaminista Recep Tayip Erdogan, ta yadda za a bada damar yaki da cin hanci da rashawa, da ke ci gaba da tsananta a kasar. Ita ma Jam'iyyar adawar kasar ta bukaci Erdogan da sauran ministocin sa su sauka daga mukamansu.
An ce zanga-zangar da ta ja hankalin sassan siyasar kasar na da alaka da zargi samun 'ya'yan wasu ministoci 3, da laifin cin hanci da rashawa. Tun kuma daga ranar 17 ga watan nan, rundunar 'yan sandan Turkiyyan suka fara daukar matakan yaki da cin hanci da rashawa, inda aka cafke mutane 42 cikinsu har da wadannan 'ya'yan ministocin 3. An dai zargi wadanda aka kame ne da hannu cikin laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa ta hanyar neman wasu kwagilolin gine-gine, da halalta kudin haram, da fasa kwaurin zinare, zargin da ya yi matukar girgiza kasar ta Turkiyya.(Bako)