Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin gudanar da zabe mai zaman kansa na kasar, ya kafa cibiyoyin kada kuri'u kimanin dubu 8 a wurare da dama, za kuma a kammala kada kuri'u ne da karfe 6 na yammaci. Bugu da kari, an ce adadin masu kada kuri'un a yayin zaben na wannan karo ya kai sama da mutum miliyan 21.
Kaza lika zaben ya samu shigar bangarorin siyasa da suka hada da jam'iyyun siyasa, da kawancen jam'iyyu, da 'yan takara masu zaman kansu kimanin 280. Baya ga 'yan takara sama da dubu 9, da za su fafata a nemi kujeru 328 a sabuwar majalisar dokokin kasar.
Bugu da kari, gwamnatin kasar ta dauki tsauraran matakan tsaro masu yawa domin tabbatar da gudanar da zaben yadda ya kamata. (Maryam)