Cikin rahoton, wakilin musamman na babban magatakardar MDD mai kula da harkokin Iraq,kana shugaban tawagar Nickolay Mladebnov ya bayyana cewa, ana ganin wadannan aikace-aikacen ta'addanci da musayar wuta za su ci gaba da bata yanayin zaman karkon kasar matuka. Kuma muna fatan shugabannin kasar za su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, su kafa sabuwar gwamnati bisa tsarin mulkin kasar, dukufa wajen cimma matsayi guda wajen fitar da shirin warware batun al-Anbar yadda ya kamata. (Maryam)