A gun wani bikin kaddamar da taron kara-wa-juna-sani da aka shirya a dakin karatu na Al-Assad dake brnin Damascus , Al-zohbi ya ki amincewa da duk zargin da jami'in Turkiyya ya yi.
Al-zohbi ya ce, Turkiyya ta zargi Siriya da laifin fashewar bom din, don ta kawo kafar ungulu ga shirin kasashe Rasha da Amurka na yin taron kasa da kasa game da batun Siriya.
A ranar 11 ga wata ne, aka samu fashewar boma-bomai guda 2 da aka dasa cikin mota a birnin Reyhanli na lardin Hatay dake kudancin kasar Turkiyya, inda ke kusa da iyakar kasa tsakanin Turkiyya da Siriya, abin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 46, tare da jikkatar wasu sama da 100. Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya Muammer Guler ya ce, wata kungiyar dakaru da ke da alaka sosai da hukumar leken asiri ta Siriya ta dauki alhakin wannan hari, kuma babu alakar dake tsakanin 'yan gudun hijira da bangaren adawa na kasar da wannan lamari .(Bako)