Kungiyoyin Afirka na shirin taka rawar gani a gasar cin kofin duniya Idan an dubi tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, za a ga kungiyoyin kasashen nahiyar Afirka sun sha taka rawar gani, sun kuma taba lashe kungiyoyi masu karfi daga nahiyoyin Turai da Amurka ta Kudu, sai dai har yanzu ba su taba kaiwa ga wuce wasannin zagaye na uku na gasar ba. Cikin kungiyoyin kasashen Afirka, Kamaru a shekarar 1994, da Senegal a shekarar 2002, da Ghana a shekarar 2010, dukkansu sun taba shiga zagayen na uku da kungiyoyi 8 ke bugawa, sai dukkanin su a nan suke tsayawa, ba sa samu damar tsallake wannan zagaye. Don haka ne samun damar ci gaba ya zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, ya zama wani babban buri da kungiyoyin kasashen Afirka ke neman cimmawa.
|