140714worldcup_33
|
140714worldcup.m4a
|
Shekaru 24 ke nan da kasar ta dauki wannan kofi a karon karshe kafin na bana, kana wannan ne karon farko da kasar ta dauki kofin a matsayin dunkulalliyar kasa guda, kuma kofi na farko da wata kasar Turai ta taba dauka a gasar da aka buga a nahiyar kudancin Amurka.
Jamus ta kuma karbi kyautar kudi daga FIFA har dalar Amurka miliyan 35, yayin da aka baiwa Argentina da ta zo na biyu dala miliyan 25.
Mai tsaron gidan Jamus din Manuel Neur ne ya samu lambar zinari ta kola mafi hazaka, sai lambar yabo ta dan kwallo mafi bajimta da aka baiwa Leonel Messi na Argentina, yayin da dan wasan Columbia James Rodrigues ya karbi lambar zinari ta dan wasa mafi zura kwallo a gasar.