in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamus ta doke Aljeriya da ci 2 da 1
2014-07-01 17:16:51 cri

A daya wasan da aka buga jiya Litinin kuwa, Jamus ta doke Aljeriya da ci 2 da 1, wanda hakan ya baiwa Jamus din damar shiga jerin kasashe 8, da za su buga zagayen wasannin kusa da na kusa da karshe.

Tun da farko dai kungiyoyin biyu sun shafe mintuna 90 na zangon farko babu ci, kafin daga bisani 'dan wasan Jamus Adre Shurrle ya ciwa kungiyarsa kwallon farko, a mintuna 2 da shiga karin lokaci. Sai kuma kwallon da Mesut Ozil ya zura a ragar Aljeriya a minti na 120.

Kafin dai tashi daga wasan shi ma 'dan wasan Aljeriya Abdelmoumene ya samu damar zura kwallo guda a ragar Jamus, aka kuma tashi Jamus na da 2, Aljeriya na biya da kwallo 1. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China