in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
David Mark ya bukaci Super Eagles da ta yi kokarin doke Faransa
2014-06-30 10:15:28 cri

Shugaban majalissar dattawan tarayyar Najeriya David Mark, ya yi kira ga kungiyar kwallon kafar kasar ta Super Eagles, da ta zage damtse wajen ganin ta doke kasar Faransa a wasan da za su buga a Litinin din nan.

Mr. Mark wanda tun da farko, ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar zuwa bikin bude gasar cin kofin duniyar da ake ci gaba da bugawa yanzu haka a kasar Brazil, ya bukaci 'yan wasan Najeriyar da su sanya kwazo da himma a wasan su na gaba, kamar yadda suka faro a baya.

Shugaban majalissar dattawan tarayyar Najeriyar ya kara da cewa, nasarar Super Eagles, nasara ce ga nahiyar Afirka baki daya. Daga nan sai ya jaddada alkawarin gwamnatin tarayyar Najeriyar, na baiwa kungiyar dukkanin tallafi da kwarin gwiwa, da kuma tukuicin da aka alkawarta musu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China