in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasannin kwallon kafa ta Nijeriya ba ta dakatar da biyan kudi ga 'yan wasan kasar ba
2014-06-30 16:23:00 cri

Da misalin karfe 12 na daren Litinin din nan ne bisa agogon Beijing ne za a fafata tsakanin kungiyar Super Eagles ta Nijeriya da takwarar ta ta Faransa, a kokarin su na tsallakawa zuwa ga wasan Quarter finals. Za dai a buga wannan wasa ne a filin wasa da ke birnin Brasília, babban birnin kasar Brazil. Kafin kuma wannan wasa, kungiyoyin biyu sun riga su gana da manema labaru tare da bayyana kudurin su na lashe wannan wasa.

Kafin wannan wasa dai, da akwai wani labari maras dadi dake cewa hukumar wasannin kwallon kafar kasar Nijeriya, ta dakatar da biyan kudin bonas ga 'yan wasan na Super Eagles, lamarin da ya sanya 'yan wasan suka kauracewa yin horo da aka tsara, tare da nuna aniyar su ta kin buga wasan su da Faransa, wanda zai basu dama tsallakawa ga wasan kusa da na kusa da karshe. Sai dai babban mai horaswa da 'yan wasan Stephen Keshi ya musunta wannan zargi.

"Hukumar wasannin kwallon kafa ta Nijeriya ba ta taba dakatar da biyan albashin 'yan wasa ba. Idan muna da kudin bonas, ta na biyan mu nan da nan. Sabo da haka dai babu wata matsala da ka iya kawo illa ga wasan da za a buga a Litinin. Ba mu da matsala ko kadan kan kudin bonas. Muna da karsashi, mun shirya fafatawa a wannan wasa."

Sai dai a daya bangaren bayan kungiyar ta Super Eagles ta gama wasanta da Agentina, an soke darasin horaswa na ranar 26 ga watan Yuni. Wanda hakan ya sanya wasu hasashen cewa mai yiwuwa ne 'yan wasan Nijeriya ba su da sha'awar buga wasan na gaba. Game da haka, kyaftin din kungiyar Mikel John Obi ya yi bayani.

"A ganina, wannan dai ba wata babbar matsala ba ce. Dalilin da ya sa ba mu yi horo ba shi ne, domin muna son farfado karfin jikinmu ta hanyar hutawa, tare da nazartar wasan da muka rigaya muka buga na baya. A gaskiya wannan dai ba wani abun damuwa ba ne ko kadan. A halin yanzu dai komai ya yi daidai. Idan ba mu da wani abun tattaunawa za mu gudanar da atisaye, yanzu haka muna mai da hankali sosai kan wasan gaba, muna fatan cimma nasara."

A bangaren Faransa wadda ba a yi zaton za ta taka wata rawar a-zo-a-gani kafin fara gasar ta bana ba, a hannu guda ta samu maki mai kyau a wasannin share fage. Amma yayin da aka fara buga wasannin in-ba-ka yi bani-wuri, babban mai horaswa da kungiyar ta Faransa Didier Deschamps ya yi matukar taka tsantsan. Game da abokiyar karawarsa ta Nijeriya, Mista Deschamps ya jinjina mata. Ya ce,

"Abubuwan musamman da kungiyar Super Eagles ta Najeriya take da su sun sha bamban sosai da na kungiyar Switzerland. A ko da yaushe ina fatan 'yan wasana za su rike kwallon sosai, ina fatan 'yan wasa na za su yi matsin lamba ga abokan karawar mu. Mai yiyuwa ne za su iya cimma wannan buri a gobe, watakila ba za su iya yin haka ba. Sabo da kungiyar Nijeriya ta kware sosai wajen kariya, sabo da haka tilas ne mu yi kokarin samun dabarar magance haka."

Za a fara wasan Najeriya da Faransa ne dai da misalin karfe 1 na ranar Litinin bisa agogon Brasilia, yanayin zafi zai kasance digiri 28 da wani abu. Game da wannan yanayi, Didier Deschamps ya ce,

"Za a fara wasanmu da misalin karfe 1 na yamma ne, lokacin dai ba safai a kan yi wasa ba. A cikin 'yan kwanaki 3 da suka gabata, mun yi horo domin wannan lokaci, ciki har da sauyi kan abinci da abin sha. Akwai bambanci sosai game da buga wasa a wannan lokaci, domin yanayi yana da zafi kwarai da gaske. Na san cewa 'yan wasan na Najeriya sun fi mu juriyar wannan yanayi, ko da yake wasu daga cikin su suna wasannin kwallon kafa ne a Turai. Ban da matsalar tsanannin zafi, matsala ta biyu da nake damuwa ita ce yanayin danshin iska, ko da yake wannan matsala ba lallai ta tsananta ba, amma idan muka samu kan mu a yanayi maras dadi, to hakan na iya kawo mana illa." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China