in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin Afirka na shirin taka rawar gani a gasar cin kofin duniya
2014-06-12 19:04:17 cri

Idan an dubi tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, za a ga kungiyoyin kasashen nahiyar Afirka sun sha taka rawar gani, sun kuma taba lashe kungiyoyi masu karfi daga nahiyoyin Turai da Amurka ta Kudu, sai dai har yanzu ba su taba kaiwa ga wuce wasannin zagaye na uku na gasar ba.

Cikin kungiyoyin kasashen Afirka, Kamaru a shekarar 1994, da Senegal a shekarar 2002, da Ghana a shekarar 2010, dukkansu sun taba shiga zagayen na uku da kungiyoyi 8 ke bugawa, sai dukkanin su a nan suke tsayawa, ba sa samu damar tsallake wannan zagaye. Don haka ne samun damar ci gaba ya zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya, ya zama wani babban buri da kungiyoyin kasashen Afirka ke neman cimmawa.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne a gasar ta wannan shekara, wacce kungiya, ko kuma wadanne kungiyoyin nahiyar Afirka ne za su iya cimma wannan buri? Domin neman amsar wannan tambaya ne ya kamata mu yi bincike kan kungiyoyin Afirka da za su buga wannan gasa ta cin kofin duniya ta bana, musamman wadanda suka zo daga yankin kudu da hamadar Sahara, wato Kamaru, Ghana, Kodibwa, da Najeriya.

Cikinsu kungiyar Kamaru ta taba shiga wasannin zagayen karshe a gasar cin kofin duniya har karo 7. Wannan adadi ya shaida karfin kungiyar. Kungiyar ta fara ne daga shekarar 2002, inda Samuel Eto'o ya jagorance ta, sai dai duk da fitacciyar kwarewarsa wajen taka leda, shi ma ya haifarwa kungiyarsa matsala sakamakon saurin bacin ransa. Bayan da dan Jamus Volker Finke ya zama mai horar da 'yan wasan kungiyar a shekarar 2013, ya sha wahala a kokarin daidaita ra'ayoyin 'yan wasan kasar, ta yadda Alexandre Song da sauran kwararrun 'yan wasan kungiyar za su taya Samuel Eto'o kokari kamar yadda ake bukata.

Ban da Eto'o da Alexandre Song, wani dan wasan kungiyar Kamaru da ya kamata a mai da hankali a kansa shi ne Fabrice Olinga, wanda ke takawa kulob din Malaga na kasar Sifaniya kwallo. Dan wasan mai shekaru 18 a duniya, ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da zai halarci gasar cin kofin duniya ta wannan karo.

A nata bangaren kungiyar Ghana tana jan hankali sosai bisa karfinta, sai dai a wannan shekara wala-walar da aka yi wajen sanya kungiyoyi cikin rukunan gasar ya jefa ta cikin rukuni mai hadari dake kunshe da kasashe masu karfi da suka hada da Jamus, da Portugal, gami da kungiyar Amurka da Ghana ta taba lashewa cikin karin lokaci da aka yi a gasar karon da ya wuce ta shekarar 2010. Wannan yanayi da kungiyar Black stars ta Ghana ke ciki ya sa ake ganin zai yi wuya sosai, ta samu fitowa daga wannan rukuni.

Ita ma kungiyar kasar Kodibwa ta taba gamuwa da irin wannan yanayi a baya. Ya fara daga shekarar 2006, kungiyar karkashin jagorancin Didier Drogba da Yaya Ture, ta taba shiga zagayen karshe na gasar cin kofin duniya har karo 3, inda a karo 2 daga cikinsu aka sanya kungiyar cikin rukuni mai wuyar fitowa. Ga misali a shekarar 2006 ta zama cikin rukuni daya da Argentina, da Holland. Sa'an nan a shekarar 2010, kungiyar ta gamu da Brazil da Portugal.

Sai dai kamar yadda ake cewa 'an karya gashin tsiya', a wannan karo Kodibwa ta yi sa'a, ta zama cikin rukuni daya da Columbia, da Greece da Japan. Duk da cewa wadannan kungiyoyin da za su kara da Kodibwa su ma suna da karfi, amma idan an kwatanta da sauran kungiyoyi irinsu Brazil da Portugal, da dan sauki-sauki.

Hakan kari ne kan yadda 'yan wasan Kodibwa kamarsu Didier Drogba da Yaya Ture ke cikin wani yanayi na kokarin shaida kwarewarsu kafin su tsufa, su gaza iya nuna cikakkiyar kwarewarsu. Saboda haka dai ana hasashen cewa Kodibwa a wannan karo, na iya shaida karfin ta, tare da cimma burin da jama'ar kasar ke da shi na samun nasara.

A karshe kungiyar Najeriya, wadda ta shiga takarar lashe kofin duniya har karo 4, ta na kan sahun sauran kasashen dake nahiyar ta Afirka. Inda a shekarar 1994, kungiyar Super Eagles ta samu damar halartar gasar a karon farko, inda ta fito daga rukuninta a matsayin farko, sai dai daga bisani kungiyar Italiya ta lashe ta.

Bayan hakan an rika samun karin kwararrun 'yan wasa da yawa a kungiyar ta Super Eagles. 'Yan wasa irin su Nwankwo Kanu, Jay Jay Okocha, Sunday Oliseh, Taribo West, da Celestine Babayaro, sun sanya kungiyar Najeriya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 da ta 2002. Sai dai bayan da wadannan 'yan wasan sun shude kungiyar ta fada cikin wani yanayi na rashin karfi, inda ta kai a shekarar 2006 ta gaza samun damar halartar gasar cin kofin na duniya da ta gudana a kasar Jamus. Kan a shekarar 2010 ma kungiyar ba ta fito da wani karfi sosai ba.

A wannan karo, an sake sanya Najeriya da Argentina cikin rukuni daya, yayin da sauran kungiyoyin da Najeriya za ta kara da su suka hada da Bosnia da Herzegovina da Iran. Bisa kuma hasashen da aka yi, ana sa ran ganin Najeriya ta lashe Iran. Amma a nata bangaren, Bosnia da Herzegovina za ta yi wa Najeriya matsi a fannin tsaron gida, ganin yadda kungiyar ta ci kwallaye 30 a wasannin share fagen gasar cin kofin na duniya da ta buga kafin ta samu fitowa daga kungiyoyin nahiyar Turai, yayin da Najeriya a nata bangaren ba ta da fitattun 'yan wasan baya sosai, baya ga Joseph Yobo mai shekaru 34 a duniya, wanda ya taba takawa kulob din Everton na Birtaniya kwallo.

Sa'an nan yayin da Najeriya za ta kara da Argentina, zai yi mata wuya kwarai ta lashe wannan wasa da kungiya mai karfi daga Latin Amurka, wadda ita ma ke da lakabin 'Shaho'. Amma duk da haka, Najeriya na da damar samun maki daga wasan.

Idan har Argentina ta lashe abokan karawarta a wasanni 2 na farko, ta yadda za ta tabbatar da damar zarcewa zuwa wasanni zagaye na gaba, hakan zai bata damar samun karfin gwiwar kiyaye karfinta yayin karawar ta da Najeriya.

Tsakanin 'yan wasan kungiyar Najeriya wanda ya fi yin suna shi ne Mikel John Obi dake taka ma Chelsea leda, sauran fitattun 'yan wasan sun hada da Victor Moses na kulob din Liverpool, da Peter Odemwingie, da Shola Ameobi. Sa'an nan akwai Joseph Yobo, da mai tsaron gida Vincent Enyeama.

Mai horar da 'yan wasan kungiyar shi ne Stephen Keshi, wanda a baya ya ja gorar kungiyar wajen lashe kambin gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2013. An ce karkashin jagorancin Keshi, 'yan wasan kungiyar sun fara dunkulewa wuri guda, inda suke taka kwallo yadda mai horar da su ke bukata, akasin wasu sauran kungiyoyin nahiyar Afirka dake da fitattun 'yan wasa da yawa, amma rashin wani karfi da zai hada su waje daya yake hana su yin tasirin da ake fata. Bisa la'akari da yanayin da kugiyar Najeriya ke ciki a yanzu haka, ya sa ake ganin ita ma, za ta taka rawar gani a gasar cin kofin na duniya a bana.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China