in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Brazil ta fidda sabbin ranekun hutu na musamman domin gasar cin kofin duniya
2014-06-20 15:45:19 cri

Kamar dai yadda kowa ya sani kasar Brazil kasa ce ta wasan kwallon kafa, kuma jama'ar kasar suna da matukar kaunar wasan kwallon kafa a duniya. Bisa labarin da kafofin watsa labarun kasar Faransa suka bayar a ranar Lahadi, an ce mahukuntan kasar sun bayyana karin ranekun hotu domin baiwa jama'a damar kallon gasar cin kofin kwallon kafar dake wakana a kasar yanzu haka.

Kaza lika ana ganin daukar wannan mataki na kara bada ranekun hutu na musamman zai taimaka wajen sassauta matsalar zirga-zirgar ababen hawa a sassan kasar.

Dama dai kasar Brazil tana da ranakin hutu da yawa a ko wace shekara, in an kwatanta da sauran kasashen duniya. An ce bisa kididdiga kasar Brazil tana da ranakin hutu 9 a kowace shekara bisa doka, baya ga ranakin hutu 7, da shugabannin kamfanoni da hukumomi suka kebe, kamar ranar masu ciniki, da ranar ma'aikata da dai sauransu. Ban da wannan kuma, kasar ta na da wasu ranekun hutu na jihohi ko birane. Alal misali, birnin Rio de Janeiro yana da ranakin hutu na musamman 3.

Don haka a wannan lokaci da gasar cin kofin duniya ke gudana a kasar, yawan ranekun hutu a kasar ta Brazil ya karu zuwa wani sabon matsayi.

Bisa bukatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, kasar Brazil ta zartas da dokar gasar cin kofin na duniya, inda aka daidaita ayyukan shirya gasar a dukkan fannoni. Wanda hakan ya sa mambobin majalisar dokokin kasar ta Brazil suka kara wani sabon kuduri a cikin doka, wanda ya tanaji sanya ranekun hutu na musamman domin wannan gasa.

Bisa wannan mataki a yayin gasar ta cin kofin duniya na wannan karo, za a samu hutu da yammacin ranekun da kungiyar kasar ta Brazil za ta buga wasa. Kana biranen dake daukar bakuncin gudanar da wasanni sun samu ranekun hutu nasa na daban, inda za a yi hutu a wadannan birane yayin da yake gudanar da wasanni a cikin su.

Game da hakan birnin Rio de Janeiro, da Belo Horizonte sun kara samun ranakin hutu 3, sai Cuiaba da Brasília dake da karin ranekun hutu guda hudu, yayin da kuma birnin São Paulo ya kara samun ranekun hutu 6.

Birnin Salvador dake arewa maso gabashin kasar ta Brazil daya ne daga cikin biranen dake daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin na duniya, wanda tun daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli, idan an cire ranar Asabar da Lahadi, wato ranekun hutu na kasar bisa doka, da ranar hutu na birnin, da kuma ranar hutu ta musamman ta wannan gasar, jama'ar birnin za su rika aiki a yini 4 kacal a kowane mako.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China