in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa ta fidda Najeriya da ci 2 da nema
2014-07-01 09:29:56 cri

Yanzu haka dai kungiyar kasar Faransa ce za ta buga wasan kusa da na kusa da na karshe da kasar Jamus, bayan da ta samu nasara kan kungiyar Super Eagles ta Najeriya da ci 2 da nema, a wasan zagaye na biyu da suka buga jiya Litinin.

Dan wasan Faransa Paul Pogba ne dai ya zurawa kungiyarsa kwallon farko a minti na 79 da take wasa, kafin daga bisani Joseph Yobo ya ci gidansu, kwallo ta biyu da ta baiwa Faransan cikakkiyar nasara a wasan.

Kasar Faransa dai ta dauki kofin duniya a karon farko a shekarar 1998, lokacin da ta karbi bakuncin gasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China