in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kocin Nigeriya Keshi ya yi murabus
2014-07-01 10:33:39 cri

Rahotanni na bayyana cewa, kocin 'yan kwallon kafar Nigeriya Stephen Keshi ya yi murabus sakamakon kayen da 'yan wasa suka sha a gasar cin kofin duniya wanda ya fitar da su daga gasar a ranar Litinin din nan.

Kocin wanda tsohon 'dan wasan Super Eagles ne kuma mai tsaron gida ya ce, ya yanke wannan shawaran ne sakamakon ci biyu da nema da kasar Faransa ta yi wa Nigeriya a zagayensu na biyu a filin wasan Mane Garrincha dake kasar Brazil.

Stephen Keshi dai ya karbi jagorancin 'yan wasan tun a shekara ta 2011 inda 'yan wasan suka samu nasarar cin kofin nahiyar Afrika da aka buga a bara. Yana daya daga cikin mutane biyu, shi da Mahmoud El-Gohary na kasar Masar da suka ciyo kofin gasar kwallon kafa na nahiyar Afrika lokacin da suke matsayin 'yan wasa da kuma masu horaswa.

A wani bangaren kuma magoya bayan 'yan wasan Nigeriya a Abuja, babban birnin tarayyar kasar a daren Litinin din nan sun nuna rashin jin dadinsu a kan yadda kasar ta Nigeriya ta kasa kai labari a wannan gasar kofin duniyar da ake fafatawa a Brazil.

Yawancin masu sha'awar kwallon kafar sun bayyana cewa, duk da an fara wasan yadda ya kamata, kungiyar 'yan wasan ba su natsu gu daya ba sannan akwai karanci dabaru da kuma kwarewa.

Wani mai nazarin kwallon kafa a kasar Ebere Okechukwu ya ce, an fara wasan yadda ya kamata, amma kawai rashin dabarun mai horaswa ya sa babu wani abin a zo a gani, sannan ba shi da dabara, kuma a rude yake. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China