A ran 28 ga wata, Amurka da kungiyar tarayyar Turai, sun sanar da kakabawa kasar Rasha sabon takunkumi, inda da kuma nan take Rashan ta soki daukar wannan mataki da kakkausan harshe.
A wannan rana, fadar White House ta kasar Amurka ta bayar da wata sanarwa a rubuce, wadda ke cewa, sakamakon matakin da Rasha ta dauka na kawo cikas ga halin da ake ciki a kasar Ukraine, gwamnatin kasar Amurka ta yanke shawarar ci gaba da sanya wa Rashan takunkumi, wanda ya kunshi aniyar Amurkan na haramtawa manyan jami'an Rashan su 7 amfani da kudi da kadarorinsu, tare da hana a ba su takardun Visa. Baya ga kuma haramtawa wasu kamfanonin kasar 17 yin amfani da kadarorinsu dake Amurka.
Ban da wannan kuma, ma'aikatar kasuwancin Amurka, da ma'aikatar gudanarwar kasar za su kayyade, ko kuma soke izinin fitar da kayayyakin fasahohin zamani da ke iya karfafa harkar aikin sojan kasar ta Rasha, ciki har da soke izinin da aka riga aka amince da shi a da.
A nata bangare, kungiyar tarayyar Turai ta EU kuma, cewa ta yi ta shigar da karin mutane 15 da take zargi da laifuffukan gurgunta 'yancin mulkin Ukraine, cikin sunayen wadanda ta sanyawa takunkumi. Inda ya zuwa yanzu yawan adadinsu ya kai mutane 48. Kaza lika EUn ta haramtawa kasashe mambobinta ba su takardun Visa, ko amfani da kadarori da kudinsu a dukkanin fadin tarayyar ta EU.
Sai dai game da wadannan sababbin matakai da aka dauka kan kasar ta Rasha, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergey Ryabkov ya bayyana cewa, matakai ne marasa wani amfani, kuma kasarsa za ta mayar da martani daga fannoni masu yawa. (Danladi)