Yayin bikin bude taron, shugaban babban taron MDD karo na 68 John W. Ashe ya yi jawabin cewa, babban taken ranar mata ta kasa da kasa na shekarar bana shi ne, adalcin mata shi ne bunkasuwar dan Adam, in dai ba a iya kiyaye hakkin mata da yawansu ya kai rabin al'ummar duniya tare da girmama ilminsu da kuma kwarewarsu ba, ba za a iya raya al'adu da fasahohin bil Adam yadda ya kamata ba.
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a yayin taron cewa, tabbatar da zaman daidai wa daida tsakanini maza da mata da kuma kare 'yancin mata, su ne manyan ayyukan da za su iya nuna bunkasuwar zaman takewar al'umma da kuma ci gaban kasa da kasa. Kasar Sin tana goyon bayan da a mai da hankali kan batun mata, musamman ma kan fannonin bunkasuwar tattalin arzikin mata da kuma saukaka fatara da sauran fannoni. (Maryam)