A ranar Alhamis 31 ga watan Oktoba ne aka kammala babban taron kungiyoyin mata na kasar Sin karo na 11 a babban dakin taron jama'a da ke nan birnin Beijing, inda aka yi kira ga mata da kungiyoyinsu, da su bayar da karin gudummawa ga ci gaban kasa.
Taron wanda aka shafe kwanaki hudu ana gudanarwa, a kan gudanar da shi ne bayan ko wane shekaru biyar, inda a wannan karon, babban taron ya amince da rahoton aikin da kwamitin shugabannin tarayyar kungiyoyin karo na 10 ya karanta, daga bisani aka zabi kwamitin shugabannin kungiyar karo na 11.
A jawabin da ta gabatar, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ta mika sakon taya murna a madadin majalisar gudanarwar kasar Sin, game da nasarar da babban taron ya cimma, ta kuma bukace su, da su karfafa manufofin da za su yayata daidaiton jinsi tare da tabbatar da cewa, mata sun samu dama daidai da kowa a bangarorin tattalin arziki da ilimi.
A jawabinta yayin bikin rufe taron, sabuwar shugabar gamayyar ta ACWF da aka zaba, Shen Yueyue ta bayyana cewa, kamata ya yi dukkan matan kungiyoyin kabilu da ke kasar ta Sin, su kara bayar da gudummawa, ta yadda kasar Sin za ta cimma nasarar manufofin da ta sanya a gaba. (Ibrahim)