A ranar 13 ga wata, aka rufe taron dandalin tattaunawar jama'a na kasashen renon Ingila, wanda aka shafe kwanaki 5 ana yinsa a kasar Sri Lanka.
A lokacin taron, an bayar da wani rahoto inda a ciki aka yi kira ga mambobin kasashen renon Ingilan da su tabbatar da samun daidaici a tsakanin maza da mata, da kare mata, da yara mata su raya kansu, da kuma ba mata 'yancin nuna kwarewarsu.
Kuma rahoton ya jaddada rashin amincewar shi da nuna karfin tuwo da cin zarafin mata, ya kamata a kare iko da moriyar mata a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da zaman al'umma, da kuma kiwon lafiya da dai sauransu.
Taron dandalin a wannan karo, gwamnatin kasar Sri Lanka da asusun ba da lamuni na kasashen renon Ingila ne suka shirya tare, bisa makasudin samar da dama ga kungiyoyin jama'a da gwamnatoci da su yi shawarwari da juna.(Danladi)