Liu Jieyi wanda ya bayyana hakan yayin zaman muhawarar kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya dongane da harkokin mata a ranar Jumma'a 18 ga wata ya kara da cewa, batun kare hakkokin mata ba batu ne da ke nuna ci gaban rayuwar bil'adama kadai ba, ya ce, hakan na iya alamta yiwuwar samun rayuwa ta gari, da kuma dorewar zaman lafiya a dukkanin fadin duniya.
Zaunannen wakilin kasar ta Sin a MDD ya jaddada matsayin mata da cewa, su ne ginshikin samar da dukkanin wani ci gaba a duniya, don haka ya bayyana bukatar sanya su cikin masu ruwa da tsaki, a daukacin tsare-tsaren wanzar da zaman lafiya, da ma kare aukuwar rigingimu.
Ya ce, wajibi ne kasashen duniya su daukaka matsayin mata, ta hanyar ba su damar bunkasa tattalin arzikinsu, da inganta zamantakewarsu, tare da ba su damar fada a ji, a ayyukan wanzar da zaman lafiya da samar da daidaito. (Saminu)