Babban Jami'i na na kwamitin kwararru na sojojin kasar Sin bangaren sojin ruwa,Yin Zhuo a cikin bayanin sa,yace ya kamata a kaddamar da gangamin wayar da kan jama'a akan ayyukan 'yan ta'adda a kuma hadu gaba daya a yake su.
Yin wanda har ila yau mamba ne na kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasar kasar yace wannan shirin na 'yan ta'adda da aka yi shi a tsanake ba ya da alaka da addini ko kabilanci, magana ce kawai ta ta'addanci dake da alaka da kungiyoyin ta'addancin na kasashen waje.
Kalamansa ya biyo bayan wani hari da wukake ne da 'yan neman balle jihar xinjiang suka kai ga al'umma a tashar jirgin kasa a Kunming dake kudu maso yammacin kasar Sin. (Fatimah Jibril)