Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bugawa takwaransa na kasar Sin shugaba Xi Jinping domin jajentawa tare kuma da yin Allah wadai da irin wannan laifi, ya kara da cewa, zai hada kai da kasar Sin wajen murkushe ayyukan ta'addanci.
Ban da haka kuma, ma'aikatar harkokin waje na kasar Faransa ta ba da sanarwar yin tir da harin da aka kai wanda ya jawo asarar rayuka, yayin da wasu suka jikkata, tare kuma da jaddada cewa, babu wani dalilin da zai sa a yi wannan aiki ko kadan. Kasar ta Faransa ta kuma nuna tausayawarta sosai ga iyalan wadanda harin ya shafa, tare da yin alkawarin hada kai da gwamnatin kasar Sin da jama'arta wajen yakan ta'addanci.
Ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar Amurka sun aika ma ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin sakon cewa kasar ta girgiza sosai kan harin da aka kai wanda ya kawo asarar rayuka da dama. (Amina)