An bayyana daukar karin matakan yaki da ayyukan ta'addanci a dukkanin fadin kasar Sin, a matsayin wani muhimmin mataki na baiwa rayuwar al'ummar kasar kariya, tare kuma da sake daukaka matsayin ci gaban kasar.
Mamban harkar kasar ta Sin, kuma ministan tsaron jama'a Guo Shengkun ne ya bayyana hakan, yayin zaman taro na farko don gane da yaki da ayyukan ta'addanci, da kare rayuwar al'umma da aka gudanar ran Talata 27 ga wata.
Cikin jawabin da ya gabatar, minista Guo Shengkun ya yi kira da a dauki karin matakan yaki da ayyukan ta'addanci, yana mai cewa, ya zama wajibi ga dukkanin sassan hukumomin gwamnati, su taka rawar da ta dace, wajen daukar matakai, da aiwatar da dokokin da suka shafi yaki da ta'addanci yadda ya kamata. Hakan ne kadai, a cewarsa, zai haifar da zaman lafiya da tsaron rayukan al'ummar kasa. (Saminu)