in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Beijing yana tinkarar gurbacewar yanayin iska
2014-02-25 14:47:53 cri

Ganin yadda yanayin iska a birnin Beijing na kasar Sin ya kara gurbacewa na kusan mako daya, masana'antu 147 sun dakatar da ayyukansu, wassu kuma sun rage adadin kayayyakin da suke sarrafawa a masana'antun gaba daya, ya zuwa ranar Talatan nan 25 ga wata a wani matakin da mahukuntar birnin suka dauka domin rage gurbatacciyar iska.

Mahukuntar birnin a ranar Juma'an da ta gabata suka bullo da wani tsari na shawo kan wannan gurbatacciyar iska da ta baibaye garin. A wannan ranar har ila yau, aka kara daga ma'aunin dake nuna gurbacewar iska zuwa launin ruwan goro, abin da ya tabbatar da ya kai wani matsayin tsanani na biyu a karo na farko.

A cikin masana'antun, guda 36 sun dakatar da ayyukansu, guda 75 kuma sun rage adadin kayayyakin da suke sarrafawa domin su rage yawan gurbatacciyar iskar da masana'antun suke fitarwa, sannan wassu masana'antun 36 gaba daya a don ra'ayin kansu suka rage adadin ayyukan masana'antunsu, in ji ofishin kula da tattakin arziki da yada labarai na birnin Beijing. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China