Bisa labarin da aka bayar, an ce, kungiyar al'ummar Uygur ta duniya ta nuna tababa ga kasar Sin wajen daidaita harin ta'addanci da aka yi a gadar Jinshui a filin Tian'anmen a ranar 28 ga watan Oktoban bana, inda ta yi kira da gudanar da bincike mai zaman kansa kan wannan batu, kuma ta yi korafe-korafe kan manufar da ta shafi kabilu da addini da gwamnatin kasar Sin take bi.
Game da wannan batu, madam Hua ta mai da martanin cewa, ofishin 'yan sandan birnin Beijing ya gabatar da sakamakon binciken da aka yi kan wannan hari, inda aka tabbatar da cewa, an kai wannan harin ta'addanci ne bayan shiri sosai. Irin wannan harin ta'addancin da aka yi a kan fararen hula, danyen aiki ne na yaki da bil'adam da zaman al'umma, da kuma al'adu. Shi ya sa kowane mutum da ya san ya kamata zai nuna rashin jin dadi kan wannan batu da babbar murya.
Madam Hua ta kara da cewa, ana gudanar da harkoki bisa dokoki ne a kasar Sin. Gwamnatin Sin tana ba da kariya ga hakkin al'ummar Sin bisa doka, ciki har da ikon bin addini cikin 'yanci da sauransu. Dole ne a girmama dokokin da tabbatar da tsaron zaman al'umma da kuma kiyaye hakkin bil'adam ta hanyar yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifuka. Babu wata gwamnatin kasa dake bin doka da kuma daukar alhaki da za ta kyale irin wannan aikin ta'addanci a duniya, in ji madam Hua(Fatima)