A ranar Laraba ne shugaban kasar Sin kana shugaban babbar kungiyar aiwatar da gyare-gyaren kasar Xi Jinping ya jagoranci taron farko na kungiyar, inda aka amince da dokokin aikinta da kuma mambobin rassan kungiyar guda 6.
An kafa wannan kungiyar ce bayan shawarar da aka yanke a zaman taro na 3 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 da aka yi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, a matsayin wani mataki na kara zurfafa yin gyare-graye a kasar.
Mahalarta taron na ranar Laraba, sun yi musayar ra'ayoyi, inda suka amince kan dokokin aikin babbar kungiyar, babban ofishinta da kuma kananan kungiyoyin gyare-gyare a sassa guda 6, ciki har da tattalin arziki da zamanintar da batutuwan da suka shafi kula da muhalli, doka da tsarin demokiradiya, tsarin al'adu, tsarin zaman rayuwar jama'a, tsarin gina jam'iyya da tsarin kula da yadda ake ladabtarwa.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, aikin babbar kungiyar ce ta aiwatar da dukkan matakan gyare-gyaren da aka gabatar a zaman taron jam'iyyar. Don haka, ya bukaci mahalatar taron, da su fahimci muhimmancin taron a matsayin wurin da ake yanke shawara.
Bayanai na nuna cewa, tuni dai aka fara aiwatar da jerin gyare-gyaren tun bayan zaman taron jam'iyyar, ciki har da sassauta dokar nan ta haihuwar da daya tilo da gyara kan tsarin masana'antu da rijistar wuraren kasuwanci da dai sauransu. (Ibrahim)