Cikin sanarwarsa, mista Ban ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, gami da nuna fatan alheri ga wadanda suka ji rauni don su samu sauki cikin sauri. Mista Ban ya jaddada cewa, kashe-kashen da aka yi ma jama'ar wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba ba zai samu wata hujjar da za ta zauna da gindinta ba.
A daren Asabar 1 ga wata misali karfe 9 da minti 21 bisa agogon kasar Sin, wasu mutanen da suka rufe fuskokinsu sun yi amfani da wuka wajen kai hari ga jama'ar da suke tashar jirgin kasa na birnin Kunming, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 29, da jikkatar wasu fiye da 130 zuwa lokacin da aka watsa wannan labari. (Bello Wang)