Ma'aikatar sifirin kasar Sin, ta ce, yawan matafiya dake bin hanyoyin mota a daukacin fadin kasar ya karu, da kaso 5 bisa dari yayin bikin bazarar al'ummar kasar, idan an kwatanta da makamancin wannan lokacin a bara.
Tuni dai aka yi hasashen cewa, yawan matafiyan zai kai ga mutane miliyan 433 cikin mako guda na bikin bazarar.
Duk da cewa, dusar kankara da ta fara zuba tun daga Talatar da ta gabata, na haifar da cikas ga zirga-zirgar ababen hawa, kawo yanzu ba a samu wani mummunan hadari don gane da hakan ba.
Hukumar lura da sufurin ta kuma ce, adadin matafiyan ya kai ga matsayi na kololuwa a ranar karshe ta hutun, wato ranar Alhamis 6 ga watan nan, inda bisa kididdiga yawan tafiye-tafiye a wannan rana ya kai ga miliyan 92.3, adadin da ya karu da kaso 8 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin wannan lokaci a bara.
Bikin bazarar Sinawa dai shi ne bikin al'ada mafi muhimmanci da Sinawa ke yi, wanda kuma kan ba da damar sada zumunci, da haduwar iyalai a dukkanin fadin kasar ta Sin. (Saminu)