in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin ta'addanci ga tashar jirgin kasa ta birnin Kunming dake kudancin kasar Sin
2014-03-02 09:48:20 cri

A daren Asabar 1 ga wata, misali karfe 9 da minti 21 bisa agogon wurin, wasu mutane fiye da 10 da suka rufe fuskokinsu sun kai hari  a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Kunming na lardin Yunnan dake kudancin kasar Sin, inda suka sassare jama'a da wuka abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 29 sannan wasu fiye da 130 suka raunana, bisa alkaluman da aka samu zuwa karfe 6 na safiyar ranar lahadin nan 2 ga wata.

Don kare jama'a da ba su ci ba ba su sha ba daga wannan harin, 'yan sanda sun bindige mutane 4 daga cikin maharan tare da kama 1.

Abkuwar lamarin ya janyo hankalin Xi Jinping, shugaban kasar Sin sosai, wanda nan take ya ba da umarni ga rundunar 'yan sanda da ta yi kokarin binciken lamarin, da gurfanar da wadanda aka kama da laifin gaban kotu. Sa'an nan ya bukaci a kula da jama'ar da harin ya ritsa da su, da jinyar wadanda suka ji rauni. Shugaban ya kara da cewa, ya kamata a fahimci wani yanayi mai wuya da ake ciki wajen fama da ta'addanci, ta yadda za a kara daukar takamaiman matakai don dakile ayyukan 'yan ta'adda da kare jama'ar kasar.

A nasa bangaren, ofishin watsa labarai na gwamnatin birnin Kunming, ya sheda cewa, shaidun da aka samu a wajen abkuwar lamarin sun nuna cewa, lamarin ya kasance wani harin ta'addanci ne da 'yan a-ware wadanda ke neman balle jihar Xinjiang daga yankunan kasar Sin suka aikata.

Zuwa Lahadi  2 ga wata, kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua ya watsa wani sharhi mai taken 'A yi kokarin dakile ayyukan ta'addanci', wanda ya bayyana cewa, ayyukan ta'addanci na banazanar tsarin bai daya na al'ummomim kasa da kasa gami da al'adun dan Adam, wadanda suke sheda mummunar halayyar 'yan ta'adda na kin jinin al'umma da daukacin bil Adama, don haka duk wata kasa mai tsari da doka sam ba za ta kau da ido ga ayyukan ta'addanci da wadanda suka aikata su ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China