Rahoton da ke da taken hasashen yanayin tattalin arziki na duniya a shekarar 2014, dake bayyana yanayin tattalin arziki na bana da badi, yayi hasashen cewa, GDP da Amurka za ta samu a shekarar 2014 zai karu da kashi 2.5 cikin 100, yayin da wannan adadin a kasashen yammacin Turai da Japan zai kai kashi 1.5 cikin 100.
Game da gamayyar tattalin arziki ta kasashe masu saurin samun cigaban tatttalin arziki, rahoton ya yi hasashen cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samun karuwar tattalin arziki da saurinta ya kai kashi 7.5 cikin 100 cikin wasu shekaru masu zuwa, yayin da wannan adadi a India zai karu zuwa kashi 5.3 cikin 100 a shekara mai zuwa, kuma adadin zai kai kashi 3 cikin 100 a Brazil , da kuma kashi 2.9 cikin 100 a Rasha.
A karshe rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2014, yawan hauhawar farashin kayayyaki zai kasance yadda ya kamata. Baitulmalin kasar Amurka zai rage daukar matakai na sakin bakin aljihu, kuma halin da bankunan ke ciki, zai iyar janyo rashin tabbas game da tattalin arziki na duniya.(Bako)