in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana aniyarta ta ci gaba da shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD
2013-10-31 10:23:12 cri

Manzon kasar Sin dake MDD Wang Min, ya bayyana a ranar Laraba cewa, kasar ta Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya tare da shiga a dama da ita cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Wang Min ya bayyana hakan ne a taro na hudu na kwamitin babban zauren MDD mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Manzon na Sin ya ce, ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD su ne muhimman hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, kuma sun ba da babbar gudummawa wajen sasanta rigingimu tare da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali yadda ya kamata.

Ya ce, kamata ya yi al'ummomin kasa da kasa su yayata ayyukan wanzar da zaman lafiya yayin da wasu muhimman batutuwan kasa da kasa ke kara rincabewa.

Wang Min ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi tawagar MDD ta ke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, ta mutunta muhimman manufofi guda uku, wato la'akari da kasashen da abin ya shafa, rashin nuna bambanci da kaucewa amfani da karfi yayin da suke kokarin kare kansu da kiyaye nauyin da ke wuyansu.

Bugu da kari, ya ce, kamata ya yi masu aikin kiyaye zaman lafiyar, su mutunta ikon cikakkun yankunan kasashen da abin ya shafa, mutunta dokokin kwamitin sulhu, kyakkyawar amfani da damar da MDD ta tanadar, sanya muhimmanci kan hana abkuwar rigingimu, jagoranci na gari da bayar da gudummawa wajen sasanta rigingimu cikin zaman lafiya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China