in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron bunkasa zaman lafiya tsakanin addinan kasa da kasa karo na 9
2013-11-23 20:26:51 cri
A jiya Jumma'a 22 ga wata ne aka rufe taron bunkasa zaman lafiya tsakanin addinai na kasa da kasa karo na 9. Taro na kwanaki uku wanda ya gudana a Vienna, babban birnin kasar Austria, ya baiwa mahalarta sa damar zartas da "sanarwar Vienna", wanda ta kunshi kira da karfafa ikon jama'a da kuma suka mai tsanani kan masu matsanantan ra'ayoyin addinai.

Cikin sanarwar, an bayyana cewa, gwamnatoci, da kungiyoyi da kuma al'ummomin kasa da kasa suna fatan karfafa ikon jama'a, da kiyaye mutunci, da tsaron jama'a da kuma samun 'yancin bin addini.

Babban taken taron shi ne "girmama kowa da kowa, da kiyaye mutunci, da ikon jama'a da kuma samun alheri tare". Wakilan kungiyoyin da abin ya shafa sama da 700 ne da suka halarci taro na wannan karo daga kasashe kimanin 100. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China