in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya bayyana sabbin matakan bunkasa ayyukan wanzar da zaman lafiya
2013-05-30 14:17:31 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya jinjina wa jami'an wanzar da zaman lafiya, da suka rasa rayukansu yayin da suke tsaka da gudanar da wannan muhimmin aiki, tare da bayyana sabbin matakan da ake fatan dauka, domin bunkasa ayyukan tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasashen da yake-yake suka daidaita.

Yayin da yake gabatar da sakonsa na ranar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya, wanda MDD ke gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayun kowace shekara, Ban ya ce, lokaci ne na karrama wadanda suka sadaukar da kansu ga wannan muhimmin aiki, tare kuma da wayar da kan al'umma, don gane da sabbin manufofin da a yanzu haka ake nufin aiwatarwa a wannan fage.

Babban magatakardar MDD ya yaba wa irin ci gaban da ake samu a wannan fanni a dukkanin fadin duniya, a lokaci guda kuma ya bayyana irin tarin kalubale da aikin ke tattare da shi. A cewarsa, a shekarar da ta gabata kadai, kimanin ma'aikatan wanzar da zaman lafiyar MDD 111 ne suka rasa rayukansu, yayin da kuma a tsahon shekaru 65 da fara gudanar da wannan aiki, adadin ya kai mutane 3,100.

Bugu da kari, babban magatakardar MDD ya ce, a yanzu haka akwai dakarun soji kusan 80,000, da 'yan sanda 12,500 da kuma ragowar jami'ai na kasa da kasa 17,000 dake gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya 15, a nahiyoyi 4 dake sassan duniya daban daban.

Ranar 29 ga watan Mayun ko wace shekara dai ita ce MDD ta kebe domin karrama, tare da tunawa da wadanda suka sadaukar da kansu ga aikin wanzar da zaman lafiya a fadin duniya baki daya, ta kuma dace da ranar da aka fara gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin tutar majalissar ta dinkin duniya wato a shekarar 1948, lokacin da tawagar UNTSO ta fara aikinta a kasar Falasdinu.

Taken bikin na bana shi ne "Tunkarar sabbin kalubalen ayyukan wanzar da zaman lafiya."(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China