in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin rigakafin cutar kanjamau da ke Geneva sun fara shirye-shiryen ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya
2013-11-26 11:05:58 cri
Ranar 1 ga watan Disamba, ita ce ranar yaki da cutar kanjamau ta kasa da kasa, shi ya sa, hukumar kiwon lafiya ta duniya, shirin yaki da cutar kanjamau na MDD da sauran hukumomin da abin ya shafa za su fara gudanar da shirye-shirye dangane da ranar tun daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba a birnin Geneva na kasar Switzerland, don yin kira ga gamayyar kasa da kasa da ta kara fahimta da tausayawa masu dauke da kwayoyin cutar HIV.

Babban taken ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya na shekarar bana da shirin yaki da cutar kanjamau na MDD ya tsara shi ne, kawar da nuna kyama. Babbar darektar sashen kare 'yanci, jinsi, ilimantar da al'umma da shirin yaki da cutar kanjamau na MDD Mariangela Simao ta bayyana cewa, ko da a wasu wurare, yawan mutanen da ke dauke da kwayoyin cutar HIV na samun raguwa, amma adadin mutanen ya karu a yankunan gabashin Turai da tsakiyar Asiya, inda adadin ya ninka sau biyu a Gabas ta Tsakiya da kuma arewancin Afirka idan aka kwatanta da na shekarar 2001. Ta kuma kara da cewa, ya kamata a mai da hankali kan aikin kyama ga masu dauke da kwayoyin cutar HIV. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China