Bayan kusan watanni uku da ake takadama dalilin wani jerin yajin aiki daga bangaren ma'aikatan kiwon lafiyar kasar Nijar, kungiyoyin kiwon lafiya da gwamnatin kasar Nijar sun koma teburin shawarwari a ranar Lahadi da yamma tare da cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna.
A cikin wannan yarjejeniya, bangarorin biyu sun amince da matsalar kudaden alawus da ake baiwa ma'aikatan kiwon lafiya da suka shiga yajin aiki, da kasancewa takadamar dake nasaba da matsalolin da ake samu wajen aiwatar da dokar kasafin kudin shekarar 2001.
Ta la'akari da illar wannan takadama a bangaren kiwon lafiya, bangarorin biyu sun amince da yin aiki tare domin mai do da tsanaki a bangaren kiwon lafiya na kasar. Gwamnatin kasar ta dauki niyyar mikawa majalisar dokoki a ranar 20 da wani shirin doka da ya shafi al'adar kason kudaden alfarma na kashi 35 cikin 100 da ake baiwa ma'aikatan kiwon lafiya da ba da jinya tun daga bakin ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2001. Dalilin haka ne gungun kungiyoyi ya dauki niyyar janye yajin aiki na kwanaki uku da zai soma ranar Laraba mai zuwa.
Kungiyoyin kiwon lafiyar sun gudanar da yajin aiki a watanni biyu na baya bayan nan da yaje-yajen aiki domin tilastawa gwamnati daidaita matsalar 'yan kudadensu na alawus zuwa kashi 35 cikin 100 da kuma sako mutanensu da ake tsare su bisa zargin amfani da kudin kasa ba bisa doka ba. (Maman Ada)