Kungiyar tarayyar Turai gami da kasashe membobinta sun fitar da wata sanarwa a wannan rana, inda ta jaddada alkawarin yaki da cutar kanjamau, da tsara sabon buri.
Haka kuma a wannan rana, kasar Afirka ta Kudu ta kaddamar da muhimmin shirin tinkarar cutar kanjamau na shekara ta 2012 zuwa ta 2016, inda aka bayyana cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, za'a yi kokarin rage yawan mutanen da suke kamuwa da cutar da kashi 50 bisa dari.
Dadin dadawa kuma, a nasa bangaren, sakatare-janar na MDD Mista Ban Ki-Moon ya gabatar da jawabi a ranar 1 ga wata, inda yayi kira ga kasa da kasa da su nuna kwazo wajen kawar da cutar sida.(Murtala)