in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya za ta yi amfani da sabbin matakai don kariya daga cutar SIDA
2012-08-16 13:03:58 cri
Nigeriya ta ce za ta yi amfani da sabbin matakai don kariya daga cutar sida wato HIV musamman tsakanin ma'auratan da dayansu kawai ke dauke da cutar.

John Idoko babban Darekta na hukumar kare yaduwar cutar ta SIDA na kasa wanda ya bayyana haka a wani taron da ya biyo babban taron duniya a kan cutar a Abuja a jiya laraba ya ce Kasar za ta dauki matakin amfani da TENOFOVIR wani sinadarin magani dake hana kamuwa da cutar.

Ya ce, "mun damu kwarai game da yadda za mu kawo karshen kamuwa da cutar, yanzu muna neman hanyar samun magani duk da cewar muna da tazara a gaba mu sai dai yanzu mun gano cewa kimiyya da fasaha yana matsar da mu kusa da wadannan sabbin hanyoyin magani."

Idoko ya kara da cewa kasar na bukatar ganin sabbin hanyoyin hana kamuwar da cutar, saboda ba za'a iya cigaba da samar da isashshen magunguna ga wadanda yanzu haka suke dauke da shi ba.

Ya ce abinda yasa suka fi maida hankali a kan ma'aurata da dayansu ne kawai ke dauke da cutar shi ne saboda ana da yawan ma'auratan yanzu kuma a cewar shi bincike bai nuna wani gardama ba a kan wannan sinadarin magani.

Babban Direktan ya yi kira ga al'umma da su yi kokarin canza halayyansu don gwamnati ta samu saukin yaki da yaduwar wannan cuta ta sida.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China