Stockholm ta bayyana aniyar shiga takarar daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi a shekarar 2022.
Kwamitin kula da harkokin wasannin Olympics na kasar Sweden, ya sanar a kwanakin baya cewa, babban birnin kasar wato birnin Stockholm zai nemi shiga takarar daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 mai zuwa.
A halin yanzu, birnin Beijing, da Zhangjiakou na kasar Sin, da Lvov na kasar Ukraine, da Almatu na kasar Kazakhstan da kuma Krakow na kasar Poland ne, suka riga suka sanar da neman shiga wannan takara, kana ana zaton birnin Oslo na kasar Norway, shima zai sanar da shiga takarar kafin ranar karshe ta rube shiga takarar.
Kwamitin kula da harkokin wasannin Olympics na kasar Sweden ya nuna goyon baya ga birnin Stockholm, don gane da wannan aniya ta sa, sai dai shugaban sashen kula da harkokin wasanni na kasar ya bayyana cewa, abu ne mawuyaci ga gwamnatin kasar Sweden, ta bada isasshen kudin da za a iya bukata a wannan fanni.
Kwamitin gudanarwar hukumar wasannin Olympics ta duniya, zai tabbatar da jerin sunayen biranen da suka samu iznin shiga takarar a watan Yuli na shekarar badi, kana a bayyana birnin da zai dauki bakuncin wasannin na Olympics na lokacin sanyi, na shekarar 2022 a gun cikakken taro na 127, na hukumar wasannin Olympics ta duniya da za a yi, a ranar 31 ga watan Yuli na shekarar 2015 a kasar Malaysia.
Akasarin mazauna birnin Munich na adawa da burin birnin, na shiga takarar daukar bakuncin wasannin Olympics na shekarar 2022.
To daga birnin Stockholm na kasar Sweden, sai kuma Munich na kasar Jamus, inda a kwanakin baya, aka jefa kuri'u kan bukatar birnin na shiga neman takarar daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022. Inda sakamakon kuri'ar ya nuna cewa, akasarin masu jefa kuri'un basa goyon bayan birnin ya shiga waccan takara, wanda hakan ya bayyana cewa, watakila birnin na Munich zai janye daga shiga takarar neman daukar bakuncin wasannin na Olympics na shekarar 2022.
Kididdigar da aka yi, ta nuna cewa kashi 51 cikin dari, na masu jefa kuri'un sun nuna adawarsu ga wannan batu.
Gwamnatin birnin Munich ta taba bayyana cewa, idan jama'ar birnin ba su goyon bayan birnin ya shiga takarar, ko shakka babu za a yi watsi da batun takarar. (Saminu Alhassan/Zainab)