Yan wasan Najeriya 5, na cikin jerin 'yan takarar zakaran kwallon kafar nahiyar Afirka.
Hukumar kwallon kafar nahiyar Afirka CAF, ta ce 'yan wasan Super Eagles 5, na cikin 'yan wasa 25, da zasu yi takarar zama zakaran kwallon kafa na nahiyar Afirka na shekarar 2013 da muke ciki.
'yan wasan na Super Eagles 5 sun hada da kyaftin, kuma mai tsaron gidan kungiyar Vincent Enyeama, da 'yan gaban kungiyar Ahmed Musa da Emmanuel Emenike. Ragowar su ne 'yan tsakiya John Mikel Obi da kuma Sunday Mba.
Baya ga wadannan 'yan wasa 25, a cewar hukumar ta CAF, akwai kuma wasu 'yan wasan 21, da ke takarar zama zakaran kwallon kafar nahiyar ta Afirka na 'yan wasa masu buga kwallo a cikin nahiyar.
Cikin wancan rukuni na farko, baya ga 'yan wasan Najeriyar su Biyar, daga kwadebuwa kuma a kwai mai rike da wannan kambi, wato Yaya Toure, da takwarorin sa Didier Drogba, da Yao Kouassi Gervais.
Har ila yau akwai 'yan wasa bibiyu daga kasashen Ghana, da Masar, da Cape Verde da kuma Algeria dake cikin wancan rukuni na farko.
Sai kuma 'dan wasa daidaya, daga kasashen Senegal, da Kenya, da Burkina Faso, da Mali, da Habasha, da Guinea, da Kamaru, da Morocco da kuma Gabon.
A rukuni na Biyu kuwa, wato na 'yan wasan dake buga kwallo a cikin nahiyar ta Afirka, akwai dan wasan Masar Mohamed Aboutrika, da na Najeriya Sunday Mba.
Bisa jimilla, cikin wannan rukuni mai kunshe da 'yan wasa 21, akwai 'yan wasan kasar Tunisiya su Hudu, sai kuma 'yan wasa uku uku daga Kamaru, da Masar da kuma Afirka ta Kudu. Ragowar sun hada da 'yan wasan Habasha Biyu, da 'yan wasa Kwadebuwa, da Tanzaniya, da Zambiya, da Janhuriyar dimokaradiyyar Congo da kuma Najeriya daidaya.
Kamar dai yadda hukumar ta CAF ta ayyana, za a yi bikin bayana zakaran na Afirka ne daga wadannan rukunoni guda biyu, a ranar Alhamis 9 ga watan Janairun shekara mai zuwa a birnin Ikkon jihar Legas ta tarayyar Najeriya, yayin bikin hadin gwiwar hukumar ta CAF, da kamfanin sadarwa na Glo.
Bolt, Fraser-Pryce win IAAF annual award.
An bayyana sunayen 'yan wasan tseren fanfalakin nan 'yan asalin kasar Jamaican Usain Bolt, da takwararsa Shelly-Ann Fraser-Pryce, a matsayin 'yan wasan motsa jiki mafiya hazaka na bana.
Shi dai Bolt, wannan ne karo na Biyar da ya samu nasarar lashe wannan kambi, yayin da ita kuma Fraser-Pryce, ta dada samun wannan nasara a karo na 5. Tuni dai 'yan wasan 2 suka karbi kofunan da hukumar IAAF ta basu, bayan wannan nasara da suka samu, yayin wani kasaitaccen biki da aka gudanar, karkashin jagorancin cibiyar lura da wasannin motsa jiki ta kasa da kasa IAF.
Ance baya ga kofunan da 'yan wasan Biyu suka karba, kowannen su zai karbi zinzurutun kudi har dalar Amurka 100,000.
Bolt, dan shekaru 27da haihuwa, ya taba amsar wannan kambi a shekarun 2008, da 2009, da 2011 da kuma 2012, baya ga kare kambin gudun tseren mita 100 da mita 200 da ya yi a birnin Moscow a bana, inda ya kamala gudun zagayen karshe cikin mintuna 19.66. Banda wasannin kasa da kasa, Bolt ya kuma lashe wasu gasannin da aka gudanar a Jamaica.
Itama Fraser-Pryce, 'yar shekaru 26 da haihuwa, ta sake amshe kambin ta a zangon gudun mitoci 100 da aka gudanar a birnin na Moscow, bayan ta kamala gudu cikin mituna 10.71, wanda ya kasance sakamako mafi sauri a dukkanin tsahon wannan shekara da muke ciki
Da take bayyana farin cikin ta ga nasarar da ta samu a wannan karo, Fraser-Pryce, ta ce ba koda yaushe ake kwana a gado ba, amma dai a wannan karon ta cimma nasarar da take fata.
Fraser-Pryce itace mace ta Biyu daga kasar Jamaica, da ta kai ga cimma wannan nasara, baya ga Merlene Ottey data karbi kofin a shekara ta 1990.