130912-afirka-an-kammala-zagayen-farko-na-gasar-neman-shiga-cin-kofin-kwallon-kafa-na-duniya-zainab.m4a
|
A ranar 9 ga watan nan da muke ciki ne aka kammala zagayen farko na dukkan gasannin rukuni rukunin nahiyar Afirka, na neman shiga gasar cin kofin duniya da zama gudanar a kasar Brazil a shekarar 2014 mai zuwa.
Yanzu dai kuloflika na kasashe 10 ne zasu shiga gasar zagaye na biyu, wadanda suka hada da Nijeriya, da Ghana, da Cote d'Ivoire, da Kamaru, da Senegal, da Algeria. Ragowar sune Burkina Faso, da tsibirin Cape Verde, da Masar da kuma kasar Habasha.
A cikin wadannan kungiyoyi 10, kulaf din kasar Cape Verde ya ja hankalin masu sha'awar kwallon kafa, duba da cewa Kasar ta Cape Verde karamar kasa ce dake da mutane dubu 500 kacal, amma ta samu nasara kan sauran manyan kungiyoyin kasashe da suka shiga gasar har ta kai ga kasancewa a zagaye na biyu. Ita da Saliyo, Tunisia da kuma Equatorial Guinea dake rukunin B.
Kungiyar kasar Cape Verde ta fuskanci matsala da fari, cikin wasanni 3 da ta yi. Amma bayan da ta sha kashi a hannun kungiyar Equatorial Guinea a gasa ta uku da ci 3 da 4, hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta canja sakamakon wannan gasa, Inda tace Cape Verde ce ke da maki 3, yayinda Equatorial Guinea ta tashi a tutar babu, hakan dai ya boyi bayan hukuncin da FIFA ta yanke ne cewa, kungiyar kasar Equatorial Guinea ta yi amfani da wani dan wasa ba bisa ka'idoji ba.
Watakila hakan ya karfafawa Cape Verde din gwiwa, domin kuwa daga nan ne ta fara samun nasara a gasanninta na gaba. A gasa ta biyu tsakaninta da Equatorial Guinea, ta lashe gasar da ci 2 da 1, daga baya FIFA ta sake canja sakamakon gasar, inda tace Cape Verde din ta doke Equatorial Guinea da ci 3 da ba ko daya. Bayan haka, Cape Verde ta lashe Saliyo da ci daya da nema. Kuma a gasar karshe, Cape Verde ta lashe kungiyar Tunisia da ci biyu da ba ko daya, duk kuwa da cewa Tunisia na da karfi, a baya ta kuma taba shiga gasar cin kofin duniyar har sau hudu.
A sakamakon haka, kungiyar Cape Verde ta samu maki 12, ta kuma kasance ta farko a rukuninta, yayin da Tunisia ta samu maki 11, ta kuma rasa damar shiga gasar zagaye na biyu.
A ranar 7 ga wata a filin wasa na Calabar dake tarayyar Nijeriya, kungiyar wasan kwallon kafa ta Nijeriyar ta lashe kungiyar Malawi da ci biyu da nema, a rukunin karshe. Don haka, kungiyar Nijeriyar ta samu maki 12, tare da kasancewa ta farko a rukunin F, zaku ma a fafata da ita a ci gaban gasar tsakanin kungiyoyi 10, don neman samun iznin shiga gasar cin kofin duniyar na shekarar 2014 mai zuwa.