A sakamakon haka, a ranar 7 ga wata, hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Mexico ta sanar da cewa, mai horas da 'yan wasan kasar Jose Manuel, ya sauka daga mukaminsa, kuma Luis Fernando Tena, wanda ke a matsayin mai horas da 'yan wasan kasar yayin wasannin Olympics zai maye gurbinsa.
Shugaban hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Mexico Justino Compean, ya bayar da wata sanarwa a shafin internet na hukumar a ranar 7 ga wata, inda ya bayyana cewa, Mr Tena zai maye gurbin Mr Manuel, domin zama mai horas da 'yan wasan kungiyar kasar, inda zai jagori 'yan wasan kungiyar a gasanni na gaba.
A halin yanzu, kungiyar kasar Mexico ta zama a matsayi na hudu a cikin kungiyoyi shida, da suke yin wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a yankin arewaci, da tsakiyar nahiyar Amurka da Carribean a wannan karo. Akwai saura gasanni uku a nan gaba, wadanda daga cikinsu za a samu sakamako ragowar kulaflikan da zasu shiga zagaye na gaba.
Kungiyoyi uku dake kan gaba sune a karshe zasu iya samu damar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Brazil a shekara mai zuwa.
Mr Tena mai shekaru 55 da haihuwa ya taba jagorantar kungiyar kasarsa, da samun lambar yabo ta zinara a wasannin Olympics na birnin London. Tena ya bayyana wa 'yan jarida cewa, ya yi imani, da kyakkyawan fata ga 'yan wasan kungiyarsa, na samun ci gaba da nasara a gasanninsu na gaba. (Zainab)