A nasa bangaren, shugaban tawagar kasar Masar Muz Khalil ya bayyana cewa, akasarin wakilai daga kasashe masu ci gaban masana'antu suna fatan gudanar da tattaunawa kan wasu batutuwan dake cikin yarjejeniyar Cancun kawai, amma ba su son ambatar taswirar Bali.
Shugaban tawagar kasar Sin Mista Su Wei ya fadawa manema labarai cewa, kasar Sin gami da sauran wasu kasashen dake tasowa suna fatan tsara jadawalin taron ba tare da bata lokaci ba, da gudanar da shawarwari tsakanin bangarori daban-daban bisa ka'idojin taswirar Bali da yarjejeniyar Cancun. Amma akwai wasu kasashe masu hannu da shuni wadanda suke fatan kaucewa wasu muhimman batutuwan da suka shafi ma'aunin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da yarjejeniyar Kyoto.(Murtala)