in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bukaci a saurari ra'ayoyin kasashe maso tasowa kan batun sauyin yanayi
2011-07-21 15:52:55 cri

Ranar Laraba 20 ga wata, Wang Min mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD ya lura da cewa, a cikin aikin tinkarar sauyin yanayi, kamata ya yi, kasashen duniya su yi la'akari da moriyar kasashe maso tasowa tare da fahimtar mawuyancin halin da suke ciki, saboda haka a saurari ra'ayoyinsu da mutunta bukatarsu, a kuma tabbatar da alkawarin da aka yi masu ta fuskar kudi, kimiyya, fasaha da sauransu.

A wannan rana a gun taron muhawarar da kwamitin sulhu na MDD ya yi a birnin New York, Wang Min ya ce, a ganin yawancin kasashe maso tasowa, shigar kwamitin a taron tattauna batun sauyin yanayi ba zai taimakawa kasashe daban-daban wajen tinkarar matsala ba, kuma da kyar a kawo amfani ga kasashe maso tasowa, hakan ya sa, ya nemi kwamitin da ya fahimci kuma ya girmama irin wannan damuwarsu.

Wang Min ya ce, kwamitin ba shi da fifiko wajen tinkarar sauyin yanayi balle matakai masu kyau. Kuma, tattaunawar da kwamitin ya yi, ba ta da amfani ga samun matsaya daya, balle ma ta maye gurbin shawarwarin da kasashe mambobi 193 suka yi bisa shirin yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China